Hausa May/June 2015

Question 2

            Bayyana yadda ake furta /t/
           Explain the articulation of the consonant /t/

     

Observation

The question above is on phonology, candidates were required to explain the articulation of the  consonant /t/ in terms of place, manner and position of the glottis.
Thus:
Yadda ake furta /t/
A bangaren gurbin furuci, tsinin harshe ne yake haduwa da hanka su samar da sautin. Ana kiran wannan sauti bahanke ko dan hanka.

A yanayin furuci kuwa, mafurta kan hade da juna ne ta yadda mafitar iskar za ta toshe. A nan, iskar ba za ta iya ficewa ba har sai mafurta sun saki juna. A dalilin wannan dakatawar iska ake kiran sautin tsayau .

A wajen tantanin makwallato kuma, makwallaton yakan kasance a bude ne a lokacin da ake furta wannan sauti. Don haka, iskar furuci tana wucewa salun’alun ne ba tare da tantanin makwallato ya haddasa karkarwa ba. Don haka,/t/ sauti ne maras ziza.

Few candidates attempted the question and their performance was poor.