Hausa May/June 2015

Question 7

    Yi takaitaccen bayanin ‘yan kama


Observation

Above is a question from the book Kowa Ya Sha Kiɗa (Oral poetry). Candidates were required to explain the people (singers) ‘yan kama, their background, their way of life and the type ofsong they compose.
Thus:
          ‘Yan kama ana zaton asalinsu makadan fada ne, wadanda suke cikin wawayen sarki masu ba shi dariya. Daga baya ne suka  mayar da kidansu ya hada har da wadanda ba sarakai ba. Sukan ba mutane dariya ta wajen shigarsu da ayyukansu da wakokinsu. Sukan sa tufafin gargajiya wajen shigarsu, wani lokaci har da rawani.

          Haka kuma, sukan yi damara a kan babbar riga sannan su rataya takobin icce kamar jarumai, su kuma rataya gafakar malamai, kana a dayar kafadar su rataya ganga. Sukan tsayar da gemu kuma su bar toliya a kai.

          ‘Yan kama sanannu ne wajen kwaikwayon wakoki da addu’a da karatun malamai. Misali:
          Allah ya tsare mu da mugun ji da mugun gani.
          Mugun ji dai kana zaune ka ji an ce kaza ta zubar maka da fura. Mugun gani kuwa a sa sanwar tuwo a gidanka a fara talge, tukunyar ta fashe….

  Candidates’ performance in this question was good.