Hausa May/June 2015

Question 9

    Bayyana yadda Danduna da Wakale suka ci ribar zaman tare a Danganawa.


Observation

The question above was taken from  the book  Nagari Na Kowa.  Candidates were expected to explain what Danduna and his wife Wakale benefited from their stay in Danganawa town.
Thus:

          Sana’ar Danduna ita ce noma. Yakan yi aikin gona tare da matarsa wakale. Baya ga aikin gona yakan yi sakar tabarma da tufkar igiya yana sayarwa a duk lokacin da babu aikin gona. Wakale take yin abinci da sauran aikace-aikacen gida, sannan kuma tana kiwon ‘yan dabbobi da kaji don biyan kananan bukatu. Sun zauna fiye da shekara ashirin babu wanda ya taba ji ko ganin wani abu ya faru a tsakaninsu. Dalilin haka kuwa, shi ne sun yarda da junansu kuma suna son junansu.

          Wakale tana tattalin kayan mijinta ta yadda wanda ya gani sai ya yi zaton irin kissar mata ce don ta sami tagomashi. Takan nuna wa mijin cewa ta san samu kuma ta san rashi, don haka duk abin da ya kawo, kome kankantarsa, ba ta raina masa. Shi kuma Danduna da ya ga yadda take biye da shi sau da kafa sai ya rika yin iyakar kokarinsa don ya kyautata mata.

Saboda haka hakuri da abokin zama shi yakan sa a ci ribar zama tare.

Candidates’ performance in this question was poor. This could be attributed to candidates not studying the text.