Hausa WASSCE (SC), 2018

Question 12

Yi taqaitaccen bayani a kan zaman gandu.

Observation

The question above is on Customs and Institutions (Al’ada), candidates were required to explain briefly the traditions of living in an extended family.

 

Thus:

 

Zaman gandu shi ne zama na Bahaushe na asali, inda yake zaune a cikin babban gida tare da magidanta da yawa, kuma kowanne da yankinsa a gidan, tare da iyalinsa a qarqashin shugabancin uban gandu.

A irin wannan zama akwai shugaba guda xaya tal, wanda duk abin da ya ce ya zauna. Idan ya yanka, ta yanku, ba ta tashi.wannan ya kan kasance dattijo mafi tsufa a gidan. A cikin irin wannan gida, ana iya samun magidanta da yawa a qarqashin tsohon. Shi ne mai ba da umurni da rarraba aiki a gidan , kuma shi ne mai kula da haxin kan gidan ko gandun. Idan yara sun isa aure, shi ne wanda zai haxa su auren ko suna so, ko ba su so.

Haka kuma shi ne mai warware duk rigingimun da suka taso a gandun, ya yi shari’a a zamansa na alqali. Idan ya yanke hukunci ya yanku kenan. Sukan yi komai nasu gaba xaya. Misali, lokacin damina, sai duk su haxu su tafi gonarsu ta gandu, su nome ta, sannan kuma a koma ga na sauran ’yan’uwa. A taqaice, wannan irin zama ne na cuxe-ni-in-cuxe k, da kuma lumana, babu qiyayya da gaba.

 

The candidates were expected to explain the following points:

Ma’anar Zaman Gandu;

Tsarin Zaman Gandu;

Ayyukan shugaba ko uban gandu irin su:

Shugabancin gida;

Alqalanci a gida (shari’a);

Rarraba ayyuka;

Qulla zumunci da auratayya; da sauransu.

 

Candidates’ performance on this question was encouraging.