Hausa WASSCE (SC), 2018

Question 13

 

(a) Zayyana muhimmancin sana’o’in gargajiya guda biyu.

(b) Nuna gwanintar waxannan:

(i) Mahauta

(ii) Maharba

(iii) wanzamai


Observation

This question is on culture also, and the candidates were expected to explain on the importance of any two traditional occupations, in (13a) and to describe the expertice of the traditional occupations listed in (13b).

 

The following responses were expected:

 

i. mutum yakan zama wanda ake gimamawa idan yana da sana’ar yi.

ii. Rashin sana’a na iya sa mutum ya rasa mata.

iii. Tana sa mutum, ko gida, ko unguwa, ko gari ya yi suna ko ya shahara.

iv. Tana kawo ci gaban al’umma.

v. Tana raya al’adu.

vi. Tana sa dogaro da kai.

vii. Tana bunqasa tattalin arzikin qasa.

i. Mahauta :

Suna nuna gwanintarsu a wajen al’adarsu ta hawan qaho tare da sarrafa dabba kome faxanta. Haka kuma suna nuna gwanintarsu a fagen dambe, wani lokaci ma har da tauri. Har ila yau, sun qware a fagen baqar magana.

ii. Maharba :

Suna nuna gwanintarsu ta wajen ba da maganin daji da dafi da kau-da-bara da sagau da xaurin dawa da fasa-taro. Haka kuma, sarkin maharba kan yi waibuwa, domin nuna qwarewa ta vacewa ko canza siffa.

iii. Wanzamai :

Suna nuna gwanintarsu wajen ba da maganin kashe kaifi da na aska da maganin valli-valli. Haka kuma, wanzamai kan yi waibuwa kamar sakar wa mutum quraje a jikinsa ko makamancin haka, domin nuna qwarewa.

Candidates’ performance on this question was good.