OBSERVATION
The question is also on grammar and the candidates were expected to define an ambiguous sentence and to construct five examples of an ambiguous sentence.
Thus:
Jimla Mai Harshen Damo, jimla ce wadda ta kunshi ma’ana fiye da daya. Irin wannan jimla tana iya kasancewa mai aikatau ko maras aikatau.
Misalai na Jimla Mai Harshen Damo :
- Yaron ya koma – (ya rasu ko kuma ya koma inda ya fito)
- Baki gare shi – (babban baki ko iya magana)
- Ban ga kwado ba (na ruwa ko na makulli ko na riga)
- Audu zai ba da dwarya – (kwara dari ko ta duma)
- An saya mata turmi – (na daka ko na atamfa)
- Audu ya sayar mata da littafi – (nata ya sayar ko nasa ya sayar mata)
- Binta ta kama wa Audu agwagwa – (kamu na hannu ko na ciniki)
Candidates’ performance on this question was fair.