The question is on phonology and candidates were required to explain how any two of the above sounds are articulated and further show their points of articulation.
Thus:
a. Yayin furucin /m/, leɓen sama da na ƙasa ke haɗuwa su rufe rif, sai su tare iskar huhu mai fitowa waje, daga nan sai su saki juna iskar ta fita ta hanci. Haka kuma tantanin maƙwallato yana kaɗawa ya samar da ziza. Don haka,/m/ - baleɓe ɗan hanci mai ziza.
b. Yayin furucin /t/, tsinin harshe ke haɗuwa da hanƙa, sai su tare iska na ɗan lokaci, sannan su saki juna iskar ta fice. Amma kuma, tantanin maƙwallato kan saki iska ta fice ba tare da karkarwa ba. Don haka, /t/ - bahanƙe tsayau maras ziza ne.
c. Yayin furucin /l/, tsinin harshe ke haɗuwa da hanka. Mafurta kan toshe mafitar iska na ɗan lokaci kaɗan kafin su ware, iskar ta fice ta gefen harshe. Don haka, /l/ bahanƙe ɗan jirge mai ziza.
d. Yayin furta/g/, doron harshe ke haɗuwa da hanɗa su datse iska, sannan ta fice tare da karkarwar tantanin maƙwallato . Don haka, /g/ bahanɗe tsayau mai ziza ne.
Few candidates attempted the question and their performance was poor. |