|
Question 8
|
Bayyana yadda ake yin wasan tahen “Zuciyar mai tsumma”
|
_____________________________________________________________________________________________________ |
Observation |
This question was taken from the book Wasannin Tashe (Oral Drama). Candidates were required to explain how the play Zuciyar mai tsumma is staged.
Thus:
(8) Tashen zuciyar mai tsumma, tashe ne na yara maza. Yara kimanin shida ke
yin wannan tashen. Ɗaya daga cikinsu zai yi shigar tsummokara, ya shafa baƘin tukunya ko zargina a fuskarsa ya wuce gaba saura na biye. Idan sun je wurin da za su yi tashen, sai mai tsummokaran ya tsaya wuri guda ya yi shiru. Ɗaya daga cikinsu zai sa waƙa, sauran yara suna amsawa, kamar suna yi masa zambo.
Waƙa: Zuciyar mai tsumma
Amshi: A kusa take
Waƙa: Tumbuna yau salla
Amshi: A kusa take
Waƙa: Zuciyar mai tsumma
Amshi: A kusa take
Waƙa: Malam ka sani kuwa?
Amshi: A kusa take
----------------------------------
----------------------------------
-----------------------------------
Haka za su ci gaba da yi har sai an ba su sadaka.
Few candidates attempted the question and their performance was fair. |
|
|
|