Question 10
Tir da ke da hali naki, Kunge-kunge irin naki,
Zai duhunta makwancinki, Kin ki bin mahaliccinki,
Alkawar nasa kin yada.
(a) Daga wace waka aka ciro wannan baiti?
(b) Mene ne jigon wakar?
(c) Kawo kalmomi kwatankwacin wadanda aka ja wa layi ta fuskar ma’ana.
(d) Yi takaitaccen bayanin wannan baiti.
Observation
The stanza above was taken from the book Ciza Ka Busa (Written poetry) and the candidates were expected to identify the song where the stanza was taken, the theme of the song the meaning of the underlined words and to give a brief explanation of the stanza.
Thus:
(a) Daga wakar al’adun gargajiya aka ciro baitin.
(b) Jigon wakar shi ne gargadi.
(c)i. Kunge-kunge = Shige-shige, kutse-kutse
ii. Makwancinki = Kabarinki, kushewarki
(d) Wannan baiti yana yin tir ne da mata masu halin yawace-yawace inda ya ce sun ki bin dokokin mahaliccinsu kuma sun saba alkawarin da suka yi da shi, lallai wadannan dabi’u za su jawo masu duhun kabari.
Candidates performed poorly in this question.