Hausa May/June 2015

Question 4

          (a) Me ake nufi da a’antawa?

    (b) A’anta wadannan jumloli:
              i.        Akwai ruwa a rijiyar.
              ii.       Mu muka saya jiya.
              iii.       Takan zo kullum.
              iv.      Ka fito da wuri.
              v.       Na rubuta takarda.
              vi.      Ya isa haka nan.
              vii.      Suna cikin gida.
              viii.     Ka zauna da kyau.
    ix.       Audu yaro ne.
              x.       Ga kudi.

    (a) Define Negation.
    (b) Negate the above sentences.

Observation

The question above is on grammar, and candidates were required to negate the above sentences that were constructed in positive form.
Thus:

(a)      A’antawa tana nufin kore ma’anar zance ta I, wato ta koma ta a’a. Misali, Gida ne, jumla ce mai amsa cewa I, shi ne. Ana iya kore wannan jumla ta hanyar kara ba a farko da kuma wata ba a karshen. Misali, Ba gida ne ba ko ba gida ba ne.

(b)   i. Babu/ba ruwa a rijiyar.
ii. Ba mu muka saya jiya ba.
iii. Ba takan zo kullum ba/Ba kullun takan zo ba.
iv. Kada ka fito da wuri.
v. Ban rubuta takarda ba.

  Many candidates attempted the question and their performance was encouraging.