Question 5
- Me ka fahimta da dafa-keya?
- Kera kalmomi biyu-biyu da wadannan:
- –awa;
- –ai;
- –una;
- –uka;
- –aye.
(a)Define a suffix.
(b)Create two words each from the above suffixes.
Observation
The question above is also on grammar and the candidates were required to define a suffix and create two words each from the given suffixes
Thus:
- Ɗafa-ƙeya ƙari ne da ake yi a ƙarshen saiwar kalma domin a samar da wata kalma mai ma’ana. Misali ana iya ƙara ɗafin ‘i’ a ƙarshen saiwar kalmar sara wadda ita ce sar a sami sari. Haka kuma ana iya ƙara ɗafin -aye a ƙarshen saiwar kalmar hannu a sami hannaye.
- (i) -awa
Katsina = Katsinawa
Hausa = Hausawa
(ii) -ai
Malam = Malamai
doki = dawakai
(iii) -una
allo = alluna
daki = dakuna
(iv) -uka
tsauni = tsaunuka
kwano = kwanuka
(v) hannu = hannaye
Buzu = Buzaye
Few candidates attempted the question and their performance was fair.