Hausa WASSCE (PC), 2019

Question 13

 

Mece ce gara a sha’anin aure?a.

Observation

 

Candidate is required to explain what is meant by feast in marriage.
The following explanation should be considered as relevant:

 

Gabatarwa:
Garar aure wasu kayayyakin abinci ne da akan kai wa ango da amarya bayan an gama shagalin biki. Gara ta qunshi duk waniirin kayan abinci da iyayen amarya suke da qarfin saye, kamar su buhunan gero, da dawa, da masara, da shinkafa, da taliya da nakiya da daddawa, da man shanu, da man gyaxa, da manja da kuma kayan haxi kamar; gishiri, da yaji, da kayan qanshi. A wasu wuraren ma akan haxa har da kuxi.
Muhimmancin Gara:
- Tana kawo kima ga iyayen amarya;
- Tana kare martabar amarya a gidan miji;
- Tana qara danqon soyayya tsakanin ango da amarya;
- Tallafawa ce ga sabbin ma’aurata;
- Kyakkyawar al’ada ce, da sauransu.

 

Candidates’ performance in this question was very good.