Question 3
Kawo hanyoyin da ake nazarin wasula tare da misali uku-uku daga kowanne.
Observation
The question is on phonology and the candidate is required to explain the steps for the study of Hausa vowels and give three (3) examples of each step. The following explanation are expected to be presented:
Hanyoyin nazarin wasula:
Ana nazarin furucin wasula ne ta hanya biyu; tsayi da kuma siga.
(i) Tsayi: Tsayi na nufin tsawon lokacin da ake xauka wajen furucin wasali. Wani wasalin dogo ne, wani kuma gajere. Dogon wasali shi ne wanda ake jan lafazinsa wajen furuci. Gajeren wasali kuwa, ba a jan lafazinsa.
Ga misali:
(ii) Siga: Sigar furucin wasula ta dogara ne a kan abubuwa guda biyu; matsayin harshe da kuma matsayin levva.
Dangane da harshe, ana la’akari ne da matsayin xagawarsa da kuma motsawar sassansa, wato gabansa, tsakiyarsa da kuma bayansa. Haka kuma, xagawar sama sosai, ko xagawa zuwa tsakiyar baki, ko kuma shimfixe a qasan baki. Matsayin levva kuwa ya shafi irin surar da levvan ke kasancewa ne a yayin furta wasulan. A wajen furta wani wasalin levvan kan kewaye ne, wani kuma ba sa kewayewa wasu kuma ’yan ba-ruwanmu.
Ga misali kamar haka:
Candidates’ performance in this question was not impressive.