Question 4
Bayyana alaqar da ke tsakanin suna da dirka tare da misali biyar. wanne.
Observation
The question is on grammar, and the candidate is required to explain the relationship between noun and stabilizer and give five (5) examples. The following explanation and examples are required from the candidates:
i. Gabatarwa:
Suna kalma ce ta nahawu da ake ambaton wani abu mai rai ko mara rai, wanda ake iya gani da wanda ba a iya gani. Misali; Abubakar, littafi, sanyi da sauransu. Dirka kuwa, kalma ce ta nahawu da ake amfani da ita don daidaita jumla da fayyace jinsi da adadi. Misali:
ne (nmj. tl.)
ce (mc. tl.)
ne (j)
ii Alaqar Suna da Dirka:
Suna da Dirka suna tafiya kafaxa da kafaxa ne a cikin jumla. A ko da yaushe Dirka na zuwa ne a bayan Suna domin fayyace jinsi da adadi.
Misali:
Hamza ne ya zo.
Awaki ne suka zubar da ruwan.
Kaza ce ta tone shukar.
Wasu mutane ne suka sace shi.
Garin ne ya yi zafi kawai.
Matarsa ce ta kawo saqon.
Rigarsa ce kawai ta yage.
Akuya ta ce wannan.
Makarantarmu ce waccan.
Many candidates attempted the question and their performance was encouraging.