Question 7
(a) Kawo misali uku na aron kalmomi a waqar baka
Observation
Above is a question from the book Kowa Ya Sha Kiɗa (Oral Poetry). The candidate was required to give three example of borrowing in oral song. The answer was expected to be relevant with the following explanations and examples
-
Aron kalmomi a waƙar baka:
Mawaƙan baka na Hausa kan yi aron wasu kalmomi daga wani harshe daban su yi amfani da su a lokacin da suke gabatar da waƙoƙinsu. Wasu daga cikin harsunan da suke amfani da su sun haɗa da Larabci da Ingilishi da wasu daga cikin harsunan Nijeriya. Babban misali a nan shi ne, a waƙar da Ibrahim Narambaɗa ya yi wa Alƙalin Moriki Abubakar, inda ya ari kalmomin Larabci kamar haka:
… Sahibul haƙƙi amale na gyanɗama,
Habu hukumul ƙali mala,
In yai magana ta kwakkwafe.
…
Haka kuma, a cikin wata waƙa, Galadiman kotso ya ce:… Allah wahidun, ya tabaraka,
Ya lillahi mai ba kowa, …Haka kuma, Adamu Ɗanmaraya Jos ya ce a wata waƙarsa:
… La’ilaha illallahu, Muhammadu Rasulallahi,
Allah ka taimaki soja, Ko gidansu ko da daji.
…Ta ɓangaren Ingilishi kuwa, ga abin da Galadiman kotso ya ce a wata waƙarsa:
… zamanin Mamman na Abashe,
Babba da yaro maza da mata,
Wajen ilmi ko’ina mun ƙaru,
Ga siniya firamare na nan,
Furobishal sakandare na nan …
A ɓangaren sauran harsunan Nijeriya kuwa, ga abin da Ibrahim Na Habu ya ce, a wata waƙarsa ta Mairo:… har Yarbawa suna faxa,
Suna faxa da bakin Yarbanci,
Faxa suke wa, wa, wa Mairo.
Inyamurai ma suna faxa,
Suna faxi da bakin Inyamuranci,
Suna faxa biya, biya, biya Mairo.
Har Fulani ma suna faxa,
Suna faxa da bakin Fullanci,
Faxa suke ware, ware, ware Mairo.
Har Barebari ma suna faxa,
Faxa suke da bakin Barbarci,
Faxa suke are, are, are Mairo.
Candidates’ performance on this question was good.