SECTION C
CUSTOMS AND INSTITUTIONS
Question 12
Yi bayanin waɗannan:
- Maƙeran farfaru
- Maƙeran babbaƙu
Observation
Candidates were required to give and interpret five traditional names. The following names and explanations should be considered as relevant:
Tanko:
Yaron da aka haifa bayan an haifi ’ya’ya mata a jere.
Kande/Delu/Dela/Dudu:
Yarinyar da aka haifa bayan an haifi ’ya’ya maza a jere.
Talle:
Yaro ko yarinyar da mahaifiyarsu ta rasu jim kaɗan bayan haihuwarsu.
Harande:
Laƙabi ne da ake yi wa yaron da aka haifa cikin kwana biyu ko uku da tsayuwar sabon wata.
Audi:
Laƙabi ne da ake wa yaro ko yarinyar da mahaifinsu ya rasu kafin a haife su.
Dikko:
Laƙabi ne da ake sanya wa ɗa namiji wanda aka fara haihuwa.
Kadarko:
Shi ne laƙabi da ake sanya wa yaro ko yarinyar da aka haifa bayan haihuwar tagwaye da Gambo.
Dogara/Bawa/Barau/Nabara:
Yaron da aka fara samu ya rayu bayan an yi ta haihuwa suna mutuwa.
Bayi/Ayashe:
Yarinyar da aka fara samu ta rayu bayan an yi ta haihuwa suna mutuwa.
Candidates who attempted this question performed very well.