The question was taken from the book Ciza Ka Busa (Written poetry) and the candidates were expected to briefly explain three wisdom found in the song harshen Hausa composed by Aliyu Aƙilu.
- akwai hikimar tattare ma’anoni wuri guda, misali, riga ‘yar tsugul sai a tattare ma’ana
a ce taggo, maratayi a kira shi jigo, ƙaƙƙarfan mutum a ce masa gago, gun saukar
fatake a ce masa zango, ɗan aike a ce jakada, abin hawa a ce masa tsani.
- akwai hikimar nuna kalmomin Hausa masu sunaye daban-daban. Misali, mage sai a
kira ta mussa, waina a ce mata masa, dole a ce mata tilas.
- akwai hikimar nuna sunan mutum da za a iya kira da wani suna kuma ma’anar ba ta
canja ba. Misali, Bawa sai a kira shi Makau, Kallamu a kira shi Musa, Hamidu a kira shi
Mamuda, Zainabu a ce mata Abu, Malam Dogo a ce masa wada, etc.
Candidates performed poorly on this question.