The question above was taken from the book Wasannin Tashe (Oral Drama). Candidates were required to explain how the play Ɗan-ɓera mai shiga rami was staged.
Tashen Ɗan-ɓera mai shiga rami, wasa ne na yara maza. Akan sami kimanin
yara bakwai ko takwas, sai su zaɓi ɗan ƙaraminsu mai wayo su daura masa igiya
a kunguru, sai wani ya riƙe ta baya. Idan sun shiga wani gida, sai sauran yaran su riƙa
cewa:
Ɗan-ɓera mai shiga rami.
Shi kuma sai ya riƙa ƙoƙarin cusa kansa cikin lungu yana cewa:
Na’am, in na shiga kar ku jawo ni.
Haka za su dinga yi har sai an ba su sadaka, sannan su bar gidan.
Few candidates attempted the question and their performance was fair.