Question 5
Kawo hanya uku na kore jumla tare da misali biyu-biyu daga kowanne
Observation
The question is also on grammar and the candidate is required to state three ways of negating a sentence and give two examples of each. The answer should be as follows:
Kore jumla:
Gabatarwa:
Kalmomin korewa su ne:
i - ba
ii - babu
iii - kada
iv - ba … ba
v - … ba … .
Misalan kore jumla:
- Ba ………. .
- Ba na zuwa.
- Ba ya cin abinci.
- Ba mu yarda.
- Ba su kulle qofa.
- Ba ya ji.
- Ba ya gani.
ii. Ba ………. ba.
- Ba zan zo ba.
- Ba yakan ganu ba.
- Ba na zo ba.
- Ba mu yi ba.
- Ba za a yi ba.
- Ba a sani ba.
- Ba za a je ba.
iii. Babu ………. .
- Babu kuxi a cikin aljihun rigarsa.
- Babu abin da ya gama ni da shi.
- Babu ma’aikata a wurin.
- Babu likitoci a asibiti.
iv. Kada ………. .
- Kada ka tafi kasuwa.
- Kada ka shiga rafi.
- Kada ku qara zuwa.
- Kada a zarge su.
v … ba … .
- Yau ba kuxi.
- Garin ba lafiya.
- Har yanzu ba abinci.
- Abincin ba daxi
Many candidates attempted the question and their performance was encouraging