Question 2
Bayyana bambancin furucin [d] da [y].
Observation
The question is on phonology, it required candidates to distinguish between the articulation of [d] and [y]. The response should be given as follows:
Furucin [d]:
kawo bayani ta yin la’akari da:
(a) Gurbin furucinsa:
ɗan hanƙa ne;
bahanƙe ne.
(b) Yanayin furucinsa:
tsayau ne;
ana tsayar da iska na ɗan lokaci idan za a furta shi.
(c) Matsayin maƙwallato:
baƙi ne mai ziza;
maƙwallato yakan tsuke a lokacin furta shi.
Furucin [y]:
kawo bayani ta yin la’akari da:
(a) Gurbin furuci:
ɗan ganɗa ne;
baganɗe ne.
(b) Yanayin furucinsa:
kusantau ko kinin wasali ne;
faɗin mafitar iska yana raguwa;
mafurta suna kusantar juna.
(c) Matsayin maƙwallato:
mai ziza ne;
maƙwallato yakan tsuke a lokacin furta shi.
Bambancinsu:
- Sun bambanta a gurbin furuci da kuma yanayin furuci.
- [d] bahanƙe ne, tsayau.
- [y] baganɗe ne, kusantau.
Few candidates attempted the question and their performance was poor.