Hausa WASSCE (SC), 2016

Question 10

Ga katti tuli-tuli,           Sai yawo a burtali,
Babu gaira babu dalili,      baa kali da tattali,
Saia ihu da dariya.

A daina yawon iska,       Gun kwadayi da raraka,
A je a dauko gafaka,      Don girma da daukaka,
A yanzu sai da gaskiya.

 

(a) Daga wace waka aka ciro wadannan baitoci?
(b) Mene ne jigon wakar?
(c) Kawo ma’anar kalmomin da aka ja wa layi.

 

Observation

The stanzas above were taken from the book Wakokin Mu’azu Hadeja (Written poetry) and the candidates were expected to identify the song where the stanzas were extracted, the theme of the song and meanings of the underlined words.

Thus:

(a)  Daga waƙar Tutocin Shaihu Da Waninsu ne aka ciro baitocin.
(b)  Jigon waƙar  shi ne gargaɗi.
(c)  burtali      -    hanya
raraka         -    roƙo ta hanyar dibara
gafaka        -    jaka/littafi

Candidates performed poorly on this question.