Hausa WASSCE (PC), 2016

WRITTEN LITERATURE
RUBUTACCEN ADABI

Question 9

Bayyana abin da ya faru Tsakanin Tsigarallahu da Saluhu bayan ta dawo cikin hayyacinta.

 

Observation

The question was derived from the book KOMAI NISAN DARE. Candidates were required to explained what happened between Tsigarallahu and Saluhu after she had returned to her conscience.

Thus:
Saluhu ya ɗaura mata laya maganin warkewa daga haka sa’ar da take bacci. Da ta tashi, sai ya kai ta wajen zamansa ya ba ta ruwa ta yi wanka.

Bayan ta gama wanka, ta sa kaya ta kintsa,sai ta dubi Saluhu ta ce masa, « Allah ya saka maka da alheri. Na gode. » Saluhu ya ce mata ai hakkinsa ne ya taimake ta, in kuwa ba haka ba, Allah ba zai gafarta masa ba.

Tsigarallhu ta tambaye shi dalilin wannan kalami nasa. Ya yi mata bayani. Da ta gane ko shiwane ne, sai ta fashe da kuka ta ce, « Allah sarki ! Yanzu saluhu kai ne ka taimake ni?

» Da ya ce mata shi ne, sai ta ƙara da cewa, « Ni ɗai na gama jin kunyar duniyar nan, kuma babu abin da zan ce sai roƙan gafara a gare ka kan abin da ya afku a tsakaninmu a da. Da ma Hausawa sun ce, aikata alheri sakayyarka na wurin Allah »

 

Candidates’ performance on this question was poor. This could be attributed to inadequate study of the text.