Question 13
Kawo bayani a kan waɗannan:
- Koli
- Dukanci
Observation
Candidates were required to explain Koli (Vend) in (a) and Dukanci (leather works) in (b). The following explanations should be considered as relevant:
(a) Gabatarwa:
Ma’anar koli:
Sana’a ce ta sayar da karikitai da suka haɗa da:
abin wuya ko dutsen wuya;
basilla;
jigida;
kwalli/tozali;
kayan ƙanshi;
lilo;
matsefata;
rumi;
tandu;
ulu;
warwaro
’yan kunne, da sauransu.
(b) Gundarin jawabi:
Waɗanda suke yin sana’ar;
Wurin da ake yin sana’ar;
Matsalolin sana’ar;
Muhimmancin sana’ar, da sauransu.
Kammalawa:
Yin bayani a taƙaice.
Gabatarwa:
Ma’anar dukanci:
Sana’a ce wadda ake sarrafa jemammiyar fata domin yin abubuwa kamar:
rufa laya; maratayi
guru kube
jaka kwari
kambu tandu
takalmi burgami
gafaka warki
zabira kayan doki
garkuwa taiki
zuga-zugi guga, da sauransu.
Gundarin jawabi:
Waɗanda suke yin sana’ar;
Wurin da ake yin sana’ar;
Lokacin da ake yin sana’ar;
Matsalolin sana’ar;
Muhimmancin sana’ar, da sauransu.
Kammalawa:
Yin bayani a taƙaice
Candidates’ performance on this question was very good.