Question 4
- Rarrabe tsakanin jumla mai aikatau da maras aikatau.
- Fitar da yankin suna da yankin bayani na waɗannan jumlolin:
- Malam Bala babban attajiri ne.
- Wani malami dogo fari ya sayi hula haɓar kada.
Observation
The question is on grammar and candidates were required to distinguish between the verb sentence and non-verb sentence in (a) and identify noun and verb phrases of the sentences given in (b). The following explanation and examples are required from the candidates:
(a) Rarrabewa:
i Jumla mai aikatau ita ce jumlar da ake samun kalmar aikatau a cikinta.
Misali:
Audu yana karanta jarida kullum.
Tanko ya tafi makaranta.
Bala ya dawo daga umara.
ii Jumla maras aikatau kuwa ita ce jumlar da ba a samun kalmar aikatau a cikinta.
Misali:
Shago jarumi ne.
Korau miskilin mutum ne.
Kande mata ce tagari.
(b) i Malam Bala/babban attajiri ne.
(YS) (YB)
ii Wani malami dogo fari/ya sayi hula haɓar kada.
(YS) (YB)
Many candidates attempted the question and their performance was good.