Question 13
Yi bayani a kan uku daga cikin waɗannan:
- Zagi
- Shimfiɗa
- Ƙofa
- Uwar soro
- jakadiya
Observation
Candidates were required to explain any three of the traditional tittles listed above. The following explanations should be considered as relevant:
(a) Zagi:
Shi ne mutumin da yake:
Shigewa gaban sarki idan sarki ya fito ko yana tafiya;
Dafa wa sarki sirdi idan zai hau ko zai sauka daga kan doki;
Riƙe ragamar dokin sarki;
Riƙe butar sarki idan shantali ba ya kusa.
(b) Shimfiɗa:
Shi ne mutumin da yake kula da:
Barayar sarki;
Shimfiɗun sarauta;
Tufafin sarki da abinci;
(c) Ƙofa:
Shi ne mutumin da yake:
Tsaron ƙofar gidan sarki;
Rufe ƙofar da buɗe ta;
Bayar da izinin shiga ko fita ta ƙofar gidan sarki.
(d) Uwar soro:
Mace ce wadda ka iya kasancewa ɗayan waɗannan ga sarki:
Uwa/Mahaifiya;
Yaya/Ya;
Gwaggo;
Uwargida/Matar fari.
Aikinta shi ne:
Gaya wa sarki duk wata magana da ake shakkar faɗa masa.
(e) Jakadiya:
Mace ce wadda take:
Isar da saƙon sarki zuwa ga iyalinsa;
Isar da saƙon iyalin sarki zuwa ga sarki ko wasu.
Candidates’ performance on this question was not encouraging.