Question 2
Yi bayani a kan:
(a) Wasalin [e] da [oo]
(b) Bambancin furucin [e] da [oo]
Observation
The question is on phonology, it required candidates to explain the articulation of [e] and [oo] in (a) and distinguish between them in (b). The response should be given as follows:
- Bayanin wasula:
[e] = Wasalin ƙofa ko gaba, na tsakiya, shimfiɗaɗɗe ko maras
kewaya, gajere.
[oo] = Wasalin ƙurya ko baya, na tsakiya, zumɓurarre ko mai
kewaya, dogo.
(b) Abin da ya bambanta su:
[e] Wasali ne na ƙofa ko gaba, shimfiɗaɗɗe ko maras kewaya,
gajere.
[oo] Wasali ne na ƙurya ko baya, zumɓurarre ko mai kewaya,
dogo.
A taƙaice, sun bambanta dangane da:
- Matsayin harshe: - (gaba ko baya);
- Matsayin leɓɓa: - (shimfiɗaɗɗe ko zumɓurarre ko mai kewaya ko
maras kewaya);
- Tsayi: - (dogo ko gajeren wasali).
Few candidates attempted the question and their performance was fair.