Hausa WASSCE (SC), 2018

Question 11

 

Wace shawara Malam Inuwa da Mai-Nakada suka yanke bayan an kori Zaliha daga makaranta?


Observation

This question was taken from the book Kulva na Varna (Written Drama) and the candidates were expected to explain the decision taken by Malam Inuwa and his wife Mai-Nakada over the dismissal of their daughter Zaliha, from school.

 

Thus:

 

Bayan an tabbatar da cewa Zaliha tana da ciki a makaranta, sai aka kore ta, ta isa gida ta same su suna hira. Mai-Nakada ta tambaye ta ko an yi masu hutu ne ? Ta ce mata ba a yi hutu ba, an sallame ta ne saboda rashin lafiyar ciwon ciki da haraswa.

Da suka gane an koro ta ne saboda ciki, suka tambaye ta ta faxa masu gaskiya. Ta ce masu Alhaji Ruwan Ido ya ruxe ta, ya ce mata zai aure ta. Nan take Malam Inuwa ya zabura zai doke ta, amma Mai-Nakada ta hana shi. Ta ce masa ya dakata su gama jin yadda aka yi daga Zaliha.

Da ta qare sai Malam Inuwa ya ce zai je ya samu Alhaji Ruwan Ido, ya kai shi qara wajen Alqali domin ya vata masa ‘ya. Da Mai-Nakada ta ji haka,sai ta ce masa, ‘‘Dakata Malam, idan kana son shawara. Abin da ya fi yanzu ka lallave shi ya aure ta kawai. Amma in ka kai maganar gidan shari’a, ka ga ka nema kowa ya sani ke nan. Kai dai a yi abin cikin asiri babu wanda ya sani, sai ma a riqa cewa sonta yake yi har ya fitar da ita daga makaranta.’’ Sai ya amince da wannan shawarar, ya tashi ya nufi gidan Alhaji Ruwan Ido.

The following points should be captured:

Dalilin komowar zaliha gida daga makaranta;

Yadda iyayenta suka fahimci abin da ya faru;

Shawarar da suka yanke game da cikin zaliha; da sauransu.

 

Candidates’ performance on this question was fair.