Hausa WASSCE (PC), 2019

Question 13

 

 (a)  Mece ce maita?
(b)  Yi taqaitaccen bayani kan sarkin mayu.
(c ) Kawo magani iri biyu da sarkin mayu kan bayar.

 

.


Observation

 

Candidates were required to define witchcraft ( maita) in (a), explain briefly about sarkin mayu (kingship of witchcrafts) in (b) and to list two medications that the sarkin mayu used to render in (c). The following explanations should be considered relevant:

            (a)        Ma’anar Maita:
Wata hanya ce ta yin wani sihiri ko surkulle da zai zama sanadiyyar halakar mutum. A gargajiyar Bahaushe, maita ita ce cinye kurwar mutum har ya kai ga lalacewa ya halaka.

            (b)        Sarkin Mayu:
Shi ne wanda ke ceton al’umma daga tarkon masu maita. Asalinsa shi ma maye ne, amma shi ne wanda ya ci mutum xari ba xaya (99). Wasu kuma su ce, sarkin mayu shi ne mayen da ya ci  mutum dubu, ba sauran wani abu, sai ceto. Mayu na tsoron sarkin mayu qwarai domin da sun gan shi, sai su vuya, don kada ya ci mutuncinsu.
            Sarkin mayu na iya zubar da qanqarar maita ta maye, ya ba shi magani dole ya sha, ya amaye ta, shi ke nan ya rabu da maita. Haka kuma, sarkin mayu yakan sayar da qanqarar maita ga mai buqata, da ya haxiye ta shi ke nan ya zama maye.

             (c)        i          Maganin lasar kurwa;
                          ii        Maganin hana kamun maye;
                          iii     Maganin rashin tsoron maye;
                          iv       Maganin sambatun kamun maye;
                          v        Maganin cutar da  maye ke sa wa a cikin ciki;
                          vi     Maganin qashi ko naman da maye ya sa a cikin gyambo, da sauransu.;

Candidates’ performance in this question was good.