Hausa WASSCE (PC), 2019

Question 7

 

Bayyana waxannan dangane da jigon makaxan jama’a:

  1. Wasa kai
  2. Gargaxi

Observation

 

 

Above is a question from the book  Kowa Ya Sha Kiɗa (Oral Poetry). Candidates were  required to explain as a theme of Makaxan Jama’a,  Egocentric speech in (a) and exhortation in (b). The answer should be relevant with the following explanations and examples:

(a)       Wasa kai:
Jigo ne na makaxan jama’a, wato koxa kansu da suke yi a waqoqinsu. Sau da yawa kuma, sukan zuga kansu, su nuna ba wanda zai iya ja da su a fagen waqa. Alhaji Mamman Shata, a bakandamiyarsa akwai inda yake wasa kansa kamar haka:

            Kullum yau na fi jiya,
            Haka Allah yai ni,       
            Bana na fi bara,
            Yanzu na zama gwanki sha bara,
            Xan yaro Shata ni,
            Yau dai ba wani in ba ni ba,
            Idan akwai wane ne?
            Kuma wane ne?
            To ni Alhaji roqo shigar shi nai,
            To na shiga duk, na gagari ’ya’yan gado.

 


(b)        Gargaxi: 
Makaxan jama’a sukan yi wa jama’a gargaxi kan wani sha’anin rayuwa kamar:
                        › Tattalin abin duniya;
                        ›Yadda za a zauna da iyali lafiya;
                        › Neman ilmi, da sauransu.
Alhaji Mamman Shata ya yi wata waqa wadda yake yi wa jama’a gargaxi a kan sha’anin tattali kamar haka:

                        Kuxi a kashe su ta hanya mai kyau;
                        Ka tuna yadda ka samu kuxinka;
                        Ka sha wuya ka samu kuxinka;
                        To je ka kashe su ta hanya mai kyau.


 Candidates’ performance on this question was good.