Question 12
Yi bayani game da al’adun kaciya.
Observation
Candidates were required to explain the customs attached to circumcision. The following explanations should be considered as relevant.
Al’adun Kaciya:
Yaro yakan isa kaciya idan ya kai shekara shida ko bakwai. Akan sanar da ’yan’uwa ranar da za a yi masa kaciyar. Daga nan sai iyaye su shiga shirye-shiryen abubuwa dangane da al’adun kaciya. Al’adun sun haxa da:
- Haxa yara da dama wuri xaya; a yi masu kaciya;
- Akan yi kaciya lokacin sanyi;
- Kowane gida yana da wanzaminsa;
- Akan shirya qasaitaccen biki wanda dangin yaro da abokan arziki na birni da qauye ke halarta don yi wa yaron kaciya;
- Za a haqa gajeren rami a zaunar da yaro kusa da shi ta yadda jini zai zuba a ciki;
- Wanke wurin da aka yanke da ruwan bauri da sanya, maganin tsayar da jini, da xaurewa da guntayen karare guda uku;
- Akan ajiye qwarya inda dangin yaro da abokan arziki mahalarta ke zuba abubuwan da suka kawo na kari, kamar kuxi ko goro ko turare ko tufa don ba wanzamai.
- ’Yan’uwa kan kawo abinci iri-iri da kuxi;
- Ranar fita akan yi qasaitaccen biki tare da tara wa uwar yaro kuxin gudunmuwa;
- Akan yi wa xan kaciya biqi da nama, musamman na kaji;
- Bikin fitar kaciya:
› wanka;
› kwalliya;
› ado;
› ziyartar gidan ’yan’uwa;
› sake qasaitaccen biki, da sauransu.
Candidates who attempted this question performed well.