Hausa May/June 2015

Question 12

    Bayyana yadda ake wankan jego


Observation

The question is on Customs and Institutions (Al’ada). Candidates were required to explain how wankan jego (traditional bath done by a nursing mother) is done.
Thus:
          Yadda ake yin wankan jego
          Jego shi ne zaman da mai haihuwa ke yi da kula da jaririnta har zuwa a kalla wata biyu. A wannan lokaci ne take yin wankan jego hade da shaye-shayen magungunan gargajiya da kunun kanwa ko na sabara. Takan kuma ba jaririnta dauri da yi masa gashin cibiya har lokacin da ta fadi ta warke.

          Mai jego takan yi wanka da tafasasshen ruwa a kullum daga ranar da ta haihu har zuwa kwana arba’in (40). Da zarar ta cika arba’in sai ta dakatar da wankan safe ta rika yin na yamma kawai har zuwa kwana sittin (60). Daga wannan lokaci, sai ta daina wankan kwata-kwata.

Candidates’ performance in this question was encouraging.