Hausa WASSCE (PC), 2016

Question 10

 

Yi taƙaitaccen bayan itare da misali a kan jigon waƙar ILIMIN ZAMANI.
The question was derived from the poetry of Mu’azu Haɗeja in the book titled WAƘOKIN. Mu’azu Haɗeja.

 

Observation

In the question, candidates were required to explain with examples the Theme of the poem.
Thus:
Jigon waƙar ilimin Zamani shi ne gargaɗi ga jama’a da su rungumai limin zamani. Marubucin ya kwatanta limin zamani da gishiri, lnda ya ce :

«Gishiri in babu kai ba miya,
Ilimi mai gyaran zamani.»
Ya ci gaba da cewa, ilimi ne Ke gyara ƙasa inda ya ce, «A kau da kunya a nemi ilimi. » ya ce. « Yadda kaska ke tsotson jini haka jahiƙi ke kassara mutum. » Saboda haka, ya yi kiraga jama’a kamar haka :

 

«Maza mata ku yi azzama,
Mai gemu da yaro ƙanƙane,
Am faɗa an sake faɗa muku,
Babu hasiya ga biɗar sani.”

 

Daga nan, sai ya ci gaba da cewa

“yanzu mu ne a baya saboda sakacinmu. Domin kuwa tun kafin turawa su zo, muna da hanyar saninmu, Kuma idan ba mu tashi tsaye ba, za a haye mu a wannan zamani.” Ya yi kiran mutane da ke taƙama da masayi ko ko, da su ajiye wannan ɗabia gefe, a nemi sani domin sai da ilimi ake samun waɗannan muƙamai inda ya ce: 
“Maganar yau ni ɗan wane ne,
Sai a bar ta a nemi biɗar sani.
Ɗaukaka da mutunci duk suna,
Gun sana’ar ilimin zamoni.»

 

Ya ƙara da jan hankalin jama’a da su daina yawace-yawacen banza, su tsaya su
nemi ilimi, sannan ya kirayi shugabani da su gyara harikar ilimi da sha’anin mulki, inda yace :


«jama’a da yawa ba su farga ba,
jahiki ya ƙafa sansani.
Ya yi ɗan rimi yai shamaki
Ya yi kakari yai figini
Ya yi dagatai ya naɗa haƙimai,
Ya yi Razdan yai Di’o tuni.
Jama’ar ƙudu sun ce sun fi ƙar –
Finsa, kul ya tsaya can ya bani
Sai shi koma Arewa wurin muta –
Nan da ba su da kishin zamani”

 

Candidates’ performance on this question was not encouraging.