Hausa WASSCE (PC), 2016

Question 13

 

Bayyana biyu daga cikin waɗannan hanyoyin tarbiyya a ƙasar Hausa:
- Ladabi da biyayya
- Gaskiya da tsare mutunci
- Dogaro da kai

Observation

 

The question is on customs and institutions and candidates were required to explain any two moral attitudes out of the three that are provided in the question.

 

Ladabi da biyayya:
Wannan hanya ce ta tarbiyya a ƙasar Hausa, inda ake cusa wa yara ɗabi’ar girmama na gaba da kuma kyautata wa na baya. Akan yi waɗannan ne ta hanyar koya wa yara girmama na gaba da sassauta Magana da saurarawa a cikin natsuwa da kuma ƙin tsoma baki a cikin maganganunsu. Idan kuma sun aiki mutum, ya hanzarta ya je. Haka kuma, kauce wa babba a ba shi hanya, duk suna cikin hanyoyin ladabi da biyayya a ƙasa Hausa.

 

Gaskiya da tsare mutunci :
Wannan hanya ce ta tarbiyya a ƙasar Hausa, inda ake cusa wa yara ɗabi’ar faɗa da cikawa tare da aikata ayyuka kyawawa, da kuma kauce wa abubuwan, tir da assha, da Allah-wadai. Ana iya ganin haka a cikin karin
Maganganunsu da suƙe cewa :
- « A daɗe ana yi sai gaskiya”
- “ciki da gasƙiya, wuƙa ba ta huda shi:”
- “gaskiya dokin ƙarfe”
- “mutunci madara ne,”
- “mutunci ya fi kuɗi”

 

Dogaro da kai:
Wannan hanya ce da ake koya wa waɗanda suka tasa sana’ar da za su yi domin samun abin dogaro da kai,har a yi tanaɗin iyalin da za su biyo baya. Bahaushe bai yarda da zaman banza ba ko raggonci konuna kosala. A kullum sukan kira juna da a tashi tsaye a sami abin yi domin dogaro da kai, ba sai an jira wani ya yi wa mutum hidima ba.
Har sukan ce:
- -“Babu maraya sai rago.”

 

Candidates’ performance on the question was good.