Hausa WASSCE (PC), 2016

Question 7

 

Bayyana yadda makaɗan sarakuna suke amfani da ɗaya daga cikin waɗannan, tare da misalai biyu

- Kalmomin ban tsoro
- Kwatantawa

 

Observation

The question was derived from the book KOWA YA SHA KIDA (Oral Poetry). Candidates were required to explain how the court musicians are making use of either frightening words or simile in their songs.
Thus:

 

- Kalmomin ban tsoro
Wannan nua ce ta nuna ƙwarewa da hikima inda suke zaɓen wasu kalmomi na ban tsoro domin su burge iyanyen gidansu ko zuga su. Irin waɗannan kolmonin yawanci ba su faye ma’ana ba. Misalin kalmomin ban tsoro shi ne inda Dan ƙwairo ya ce wa sardauna:


“Na ci gari Ahmadu Garnaƙaƙi
Darzaza dai Gohe duk
Wadda kaka nuhi sai ka kai.”

Haka kuma, Galadiman kotso ya yi wa Lamiɗon kano waƙa kamar haka:

“Lamiɗo Kano Alfanda
Ko dole maza su raga ma
Damamisau hana fansa. »

- Kwataintawa
A ɓangaren kwatantawa kuwa, sukan kwatanta sarakuna da wasu manya manyan namun daji ko wasu muhimman abubuwa. Misali, Galadiman kotso ya yi wa sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi waƙa, lnda yake cewa:

«Giwa mai karya itace,
Giwanici nai cinye maharba,
Rani mai ka da guzamai,
Bacci ma, taushe mutane
Ƙowa ya san ka niƙatau.”

 

Shi kuma Alhaji Musa Ɗanƙwairo, a waƙar sarkin Daura yana cewa:

 

«Toron giwa Muhammadu na jekada,
Toron giwa Muhammadu na Mai fada,
Dutsan fashin tama na Bawo,
Dan Ɓunturawa watan sallah
Sha kallo gida da daji.”

 

Candidates’ performance on this question was poor.