Hausa WASSCE (PC), 2019

SECTION C
CUSTOMS AND INSTITUTIONS

Question 12

 

(a) Yi bayanin al’adar Bahaushe ta girmama baqo.
(b) Bayyana muhimmancinta ga al’ummar Hausawa.

Observation

 

Candidate is required to explain the Hausa custom of being pleasant to their guest in (a) and enumerate the importance of doing that among the Hausa people in (b).
The following points should be considered as relevant:

 

(a) Al’adar Girmama Baqo:
Nau’i ne na karimci da mutum ke nuna kulawa ga baqon da ya zo masa ta hanyar yi masa hidima gwargwadon hali. Ga al’ada, mutum zai xauke wa baqonsa nauyin abinci da abin sha, da wurin kwana, da makewayi, da ruwan wanka da sauran abubuwan da zai buqata a lokacin baquncinsa.
Baqunta ga al’adar Bahaushe, kwana uku ne ko abin da ya fi haka.

 

(b) Muhimmancin Karrama Baqo:
- Ibada ce;
- Kyakkyawar al’ada ce;
- Xaukaka darajar mutum;
- Kyautata mu’amala;
- Qarfafa zumunci;
- Baqo rahama ne;
- Kare mutuncin kai, da suransu.

 

Candidates who attempted this question performed very well.