|
Question 11
|
Yi bayanin irin rawar da wa?annan mutane suka taka wajen tarbiyyar ‘Yarmasugida.
(a) Malam Abdu;
(b) Tagudu;
(c) ?awayen ‘Yarmasugida.
|
_____________________________________________________________________________________________________ |
Observation |
This question was taken from the book Zamanin Nan Namu (Written Drama) and the candidates were expected to explain the role played by the above actors in the character training of ‘Yarmasugida.
Thus:
Malam Abdu
Malam Abdu shi ne mijin Tagudu kuma uban ‘Yarmasugida. Ya taimaka wajen
lalacewar ‘yarsa wato ‘Yarmasugida saboda ?in tsayawar da ya yi wajen sauke
nauyin da yake kansa na magidanci. Malam Abdu bai san cin iyalinsa ba balle shan su. Ba ya yi musu sutura balle ya saya masu abubuwan bukata na yau da kullun.
Wannan shi ya jawo ya kasa sarrafa gidansa yadda har matarsa ba ta jin maganarsa. Kuma da wannan ta yi amfani wajen ?ora wa ‘yar talla.
28
Tagudu
Tagudu ce matar Malam Abdu kuma mahaifiyar ‘Yarmasugida. Ba aza wa ‘yarta
tallar ?osai kawai ta yi ba, har ma ta taimaka wajen lalacewar ‘yar ta hanyar yi
mata hu?ubar banza ta yadda za ta yaudari samari don ta samo ku?i.
Haka kuma, ita ce ta kori ‘yarta (‘Yarmasugida) da daddare ta hanyar hana ta
abincin dare, wai don ku?in ?osai ba su cika ba. Daga nan ne ma har ?awayenta
suka sami damar jan ta zuwa dandali wajen samari.
?awayen ‘Yarmasugida
?awayen ‘Yarmasugida irin su Rakiya da Mama da ‘Yarbeguwa, su ne
suka ri?a zuga ‘Yarmasugida kuma suna nuna mata irin dabarar da za ta yi wa samari don su ba ta ku?i. |
|
|
|