The question above is on Customs and Institutions (Al’ada). Candidates were required to explain any three of the above types of marriage in Hausa culture.
Thus:
Auren Sadaka
Wannan aure ne da akasari ake yi wa budurwa. Mahaifin yarinya kan bayar da ita aure ga wani mutum, malami ko wani mai ?aramin ?arfi ba tare da ya biya sadaki da kansa ba. Yawanci ma, shi kansa wanda za a aura wa yarinyar bai sani ba, sai bayan
an ?aura auren. Ita ma yarinyar ba dole ne ta san cewa ga wanda za a aura mata ba. Irin wannan aure na da nasaba da addini. Wa?ansu sun ?auki wannan irin aure a matsayin wani nau’i na sadaka mai gudana.
Auren Buta
Wannan irin aure na kasancewa ne a tsakanin tsofaffi, wa?anda babu alamar wata sha’awa a tare da su. Wato shi mijin zai yi auren ne don ya sami wadda za ta ri?a zuba
masa ruwa a buta don yin alwala. Ita kuma za ta yi auren ne da niyyar ri?a zuba wa maigidan ruwa a buta da sauran hidimomi don ta sami lada.
Auren ?auki-sandarka
A irin wannan aure, mijn shi ne zai tare a gidan matar. Wato gidan na matar ne.
Amma a ciki suke zaune. Ana kiransa ?auki-sandarka ne saboda duk ranar da suka ?ata da juna maimakon mijin ya kore ta, ya ce ta tattara ta bar masa gida, sai dai ita ta ce ?auki sandarka ka bar mani gidana.
Candidates’ performance on this question was encouraging.
|