This question is also on Customs and Institution and the candidates were expected to explain kayan zance as it relates to marriage and kayan ?auri which relates to birth in Hausa culture.
Thus:
Kayan Zance
Wa?annan kaya ne da ake aikawa da su gidan yarinyar da ake nema da aure, idan aka tabbatar sun amince da junansu sosai.
A yanzu, akan sa kayan ne cikin akwati a kai, su kuma iyayen yarinyar za su bi
gida-gida suna nuna wa ‘yan‘uwa da abokan arziki. Akan zuba kayan shafe-shafe irin su mai da hoda da sabulu da jan-baki da ‘yan kunne da sar?a da atamfofi da sauran kayayyaki gwargwadon ?arfin arzikin manemin, wani lokaci ma, har da ‘yan ku?i.
Kayan ?auri
Bayan an kwana uku ko hu?u da haihuwa, ya danganta da abin da aka haifa, iyayen miji za su sayi kayan ?auri su kai gidan mai haihuwa. Kayan ?aurin, su ne:
?afafuwan sa ko kan sa ko na akuya ko na rago da kayan yaji da kanwa da hatsi. Bayan an gyara shi an dafa, za a ?iba wa mai jego nata, saura a rarraba gida-gida. Bayan wannan ma, akwai kunun kanwa da ake yi ana rarrabawa. Muhimmin abu ne idan matar mutum ta haihu, ya yi ?auri, har ma idan bai yi ba yakan zama abin magana.
Candidates’ performance on this question was good. |