Question 4
- Mene ne yake ƙarin haske a kan aikatau a cikin jumla?
- Kawo ire-irensa guda uku tare da misali uku na kowanne a cikin jumla
Observation
The question is on grammar, candidates were required to state what qualifies verb in a sentence in (a) and list three types of it and construct a sentence with each in (b). The following explanations and examples are required from the candidates:
(a) Bayanau ne yake yin ƙarin haske a kan aikatau a cikin jumla.
(b) Ire-irensa:
(i) Bayanau na wuri;
(ii) Bayanau na yanayi;
(iii) Bayanau na lokaci.
Misalin bayanau na wuri:
Audu ya shiga can gidan.
Yara sun tsaya a makaranta.
Ɗalibai sun zo daga Kano.
Yaron ya shiga nan gidan.
A makaranta Bala ya haɗu da Kande.
Ta ƙasa Idi ya fita.
A Legas Tanko ya zauna.
Misalin bayanau na yanayi:
Musa ya kwanta a rigingine.
Yaron ya ci jarabawa da kyau.
Malam yana tafiya a hankali.
Ragunan sun shigo a guje.
A karkace motar take tafiya.
A fusace ɗaliban suka shigo.
Da sauri Isah ya fice.
Misalin bayanau na lokaci:
Bello ya zo jiya.
An ba wa ɗalibai hutu yau.
Yaron zai koma da yamma.
Zan zo gidanka da rana.
Ɗazu suka koma makaranta.
A daminar bana an yi ambaliyar ruwa.
A wannan shekara an noma gwaza.
Few candidates attempted the question and their performance was not encouraging.