waecE-LEARNING
Hausa Paper 2, May/June 2014  
Questions: 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 Main
General Comments
Weakness/Remedies
Strength
Conclusion
Question 11

Wane darasi maigida zai koya daga wasan Malam Maidala’ilu da na ‘Yarmasugida?


_____________________________________________________________________________________________________
Observation

This question was taken  from the book Zamanin Nan Namu (Written Drama) .  Here, candidates were expected to explain the lesson to be learnt by a head of household from the plays Malam Maidala’ilu and ‘Yarmasugida.

Darasin da magidanci zai koya daga wasannin Malam Maidala’ilu da na ‘Yarmasugida,  shi ne:
Magidanci zai san muhimmancin sa yara mata makaranta tare da sa ido a kan tabbatar da cewa suna karatun a kowane lokaci.

Haka kuma, wasan yana nuna muhimmancin kula da iyali ta hanyar sauke nauyin da yake kansa na biyan dukkan bukatunsu, kamar abinci da sabulun wanka da wanki da man shafawa da sauransu.

Rashin waɗata iyali da wadannan abubuwa, zai sa maigida ya zubar da girmansa, don kuwa dole yana kallo matarsa za ta ɗora wa ‘yarsa talla, ba yadda zai yi, kamar dai yadda ya faru da Malam Abdu uban ‘Yarmasugida.

Haka kuma, a wasannin biyu, maigida zai ga yadda ƙawaye ke rushe tarbiyar da iyaye ke yi wa iya’yansu mata a sanadiyyar talla.

Illar kwaɗayin tara kayan aure ga iyaye mata.

Candidates’ performance on this question was fair.

Powered by Sidmach Technologies(Nigeria) Limited .
Copyright © 2015 The West African Examinations Council. All rights reserved.