Maigida kai zam maka…,
Kai ma wannan matarka ce,
Ruwan wanka ita za ta kai,
Sharar ɗaki ita za ta yi,
Ta tuƙa abinci ka zo ka ci,
Ta lura da yara ƙanƙana,
In kai baƙi ta kula da su,
Shin malam ko bawanka ne,
A wata nawa za ka biya shi ne?
(a) Wa ya yi wannan waƙa?
(b) Mene ne jigon waƙar
(c) Fito da abubuwa biyar na ayyukan mace ga mijinta, kamar yadda ya fito a waƙar.