Hausa WASSCE (PC), 2022

SECTION C

CUSTOMS AND INSTITUTIONS

 

Question 12

 

  1. Me ka fahimta da maganin gargajiya?
  2. Yi bayanin waɗannan magungunan gargajiyar: 
  1. Tsime
  2. Sassaƙe-sassaƙe
  3. Ƙulle-ƙulle

 

Observation

Candidates were required to explain herbs in (a) and explain the types of herbs listed in (b). The following points should be considered as relevant:

 

(a)           Ma’anar maganin gargajiya: 
Hanya ce wadda ake amfani da  itatuwa ko rubutu ko addu’a ko surkulle don samun taimako da sauƙi wajen  waraka daga cutar jiki ko neman hankali ko biyan buƙata wadda ake bi tun kaka da kakanni.

 

(b)       (i)         Tsime:

Shi ne maganin da ake haɗa itatuwa ko kaucinsu ko sassaƙen jikinsu ko wasu hakukuwa a tsima su domin a yi maganin cututtuka iri-iri.

(ii)        Sassaƙe-sassaƙe:

Su ne magungunan da ake samarwa daga jikin itatuwa don maganin shawara da daji da maganin dafi da na hauka da na tauri da hangun da ciwon haƙori da ɗan kakkare da sauransu.

(iii)       Ƙulle-ƙulle:

Su ne magungunan da ake yi ta hanyar ƙulle-ƙullen abubuwa da yin tofi a zare ko tsarkiya ko  jijiya ko gashi ko ɓawon itace a rataya su a wuya ko a kafaɗa ko a kafa ko binne a gona ko a gida ko a ɗaki ko a kasuwa da sauransu.

Candidates who attempted this question performed very well.