Question 3
Bayyana waɗannan tare da misalai:
- karin sauti faɗau
- tsayau
- wasali mai aure
Observation
The question is on phonology and candidates were required to explain Falling Tone in (a), Stop in (b) and Diphthong in (c). The following explanations and examples were expected to be captured:
(a) Ma’anar karin sauti faɗau:
Sauti ne wanda kaifinsa yake yin sama ya kuma dawo ƙasa a lokaci guda yayin furucin gaɓar da take ɗauke da shi. Misali:
râi sâssân kôrrân
mâi râssân mânjân
yâu zôbbân kyâu
yârân
(b) Ma’anar tsayau:
Yanayi ne na furuci wanda ake tsayar da iskar furuci gaba ɗayanta na ɗan wani lokaci sannan a sake ta gaba ɗaya ta fita. Misali:
[b] [d] [g]
[k] [t] [gw]
[kw] [kj] [gj]
[Ɂ] [Ɂj]
Ana kiran baƙaƙen da aka furta ta wannan yanayi tsayau.
(c) Bayanin wasali mai aure:
Wasali mai aure ko tagwan wasali shi ne irin wasalin da yake da siga biyu wajen furuci. Ana fara furucinsa da tilon wasali guda a kuma ƙare da wani tilon wasalin a lokaci guda.
Misalin wasali mai aure ko tagwan wasali:
[ai]
[au]
[ui]
Candidates’ performance in this question was not encouraging.