Question 2
Ta hanyar amfani da jadawali, nuna muhallin furucin gwaurayen wasula, sannan ka bayyana yadda ake furta uku daga cikinsu.
Observation
The question is on phonology, it required candidates to draw a diagram and indicate the places for the articulation of Gwaurayen wasula (Monophthongs) and explain the manner of articulation of any three of them. The response should be given as follows:
Jadawalin gwaurayen wasula:
Bayanin yadda ake furta gwaurayen wasula:
Wasalin [i]:
Harshe yana ɗagawa sama;
Harshe yana komawa gaban baki;
Leɓɓa sukan baje/shace;
Ana kiransa ɗan sama, gaban baki ko shatau ko kuma mai bajewa.
Wasalin [u]:
Harshe yakan ɗaga sama;
Harshe yakan tsaya a saman baki;
Leɓɓa sukan kewaye ko zumɓure ko da’ira;
Ana kiransa wasalin sama, ɗan baya ko ƙuryar baki ko kuma mai kewaye ko zumɓurau ko kuma mai da’ira.
Wasalin [e]:
Harshe yana tsayawa a gaba, a tsakiyar baki;
Leɓɓa suna baje ko su shace;
Ana kiransa ɗan gaba, na tsakiyar baki mai bajewa ko kuma shatau.
Wasalin [o]:
Harshe yana komawa baya a tsakiyar baki;
Leɓɓa suna kewayewa ko su zumɓure ko su yi da’ira;
Ana kiran sa ɗan baya, na tsakiyar baki, mai kewaya ko zumɓurau ko kuma mai da’ira.
Wasalin [a]:
Harshe yakan tsaya ƙasa a tsakiyar baki;
Leɓɓa suna wangamewa;
Leɓɓa suna kasancewa ba a baje ko kewaye ba;
Ana kiran sa ɗan ƙasa, na tsakiyar baki mai wangamewa.
Few candidates attempted the question and their performance was poor.