WRITTEN LITERATURE
RUBUTACCEN ADABI
Question 9
Bayyana matan Alhaji Gabatari a taƙaice.
Observation
The question is on the book Turmin Danya (Written Prose). The Candidates were required to briefly describe the wives of Alhaji Gabatari.
Gabatarwa:
Gabatar da Alhaji Gabatari a taƙaice;
Bayanin littafi da marubucinsa a taƙaice.
Gundarin bayani:
Bayanin matan Alhaji Gabatari kamar haka:
(i) Hajiya Dija:
Mace mai hankali da ladabi ga mijinta;
Tana da taushin magana;
Fara, kyakkyawa mai jiki;
Tana da ’ya’ya biyar;
Uwargidan Alhaji;
An mayar da ita kamar karan-bara;
A kanta Alhaji yake huce duk zafin da ya ɗauko.
(ii) Hajiya Zara:
Tana da kyakkyawar fuska;
Tana da kyan diri;
Tana da matsakaiciyar siga;
Tana da ’ya’ya biyu;
Ita take bin uwargida;
Ba ta ɗaukar wargi;
Alhaji yana shakkarta;
Ta iya cacar baki.
(iii) Hajiya Tukurima:
Buzuwa ce daga Zurgis ta ƙasar Jarni;
Tana da tattausar murya mai bugar da hankali;
Ja wur take;
Tana da hanci har baka;
Tana da fararen ido;
Tana da siririn jiki;
Tana da miƙaƙƙun ƙafafuwa;
Tana da baƙin gashi mai laushi irin na Larabawa;
Ba ta jin Hausa sosai;
Ita ce matarsa ta uku;
Alhaji yana ji da ita sosai;
’Yar talakawa ce;
Ba ta jima da zuwa Makka ba.
Kammalawa:
Yin taƙaitaccen bayani.
Candidates’ performance in this question was poor.