Question 4
- Kawo abu huɗu da suke gabatar suna a cikin jumla
- Ba da misali biyu na kowanne a cikin jumla.
Observation
The question is on grammar and candidates were required to list four elements that come before noun in a sentence in (a) and construct two sentences with each in (b). The following explanation and examples were required from the candidates:
(a) i sifa
ii nunau
iii mafayyaci
iv tsigilau
v doguwar mallaka
vi warau
(b) (i) Misalin sifa:
Ƙaramin littafin ya ƙone.
Babbar riga Bala ya sayo.
Farar takarda ta ba shi.
Baƙin takalmi na saya.
Sabuwar hula Audu ya ɗinka.
(ii) Misalin nunau:
Wannan littafin ya yage.
Wannan yaron aka daka.
Waccan motar ta saya.
Waɗannan gidajen suna da kyau.
Waɗancan shanun sun ƙoshi.
Wancan mutumin baƙo ne.
(iii) Misalin mafayyaci:
Wata yarinya ta gudu.
Wani mutumi ya zo.
Waɗansu yara sun zo makaranta.
Wasu kaya aka kawo.
(iv) Misalin tsigilau:
Ɗan littafin yana da kyau.
’Yan yaran suna da wayau.
’Yar ƙwama ya saya.
Ɗan hakin da ka raina ... .
(v) Misalin doguwar mallaka:
Nawa gidan ya tsira.
Naka ɗakin babu haske.
Naki zanen ya yage.
Nasa babur ɗin sabo ne.
Nata kallabin babba ne.
Tawa ajiyar ta ƙare.
Taka motar ta wuce.
Taki jakar ta yage.
Tasa matar baturiya ce.
Tata manufar daban ce.
(vi) Misalin warau:
Ɗaya littafin ya fi tsada;
Ɗaya gidan sabo ne
Many candidates attempted the question and their performance was good.