waecE-LEARNING
Hausa Paper 2, May/June 2013  
Questions: 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 Main
General Comments
Weakness/Remedies
Strength
Conclusion
Question 13

Bayyana yadda ake yin jego

_____________________________________________________________________________________________________
Observation

The question is also on Customs and Institutions (al’ada) and candidates were expected to explain the traditional bath done by nursing mother for forty days or two months after delivery.
Thus:

  Wankan jego yana ɗaya daga cikin al’adun da Hausawa kan yi, idan mace ta haihu.
         Ana wankan jego ne domin riga-kafi daga wasu cututtuka da ka iya shiga jikin mai Jego. Haka kuma yana taimakawa wajen ƙara mata lafiyar jiki.
 
         Akan tanadi saƙesaƙi da ganyaye da saiwoyi da kwatarniya /baho da ƙatuwar tukunya ko garwa da ƙoƙo don wankan.

         Akan tafasa ruwan wankan tare da waɗannan saƙesaƙin da ganyaye da saiwoyin a cikin ƙatuwar tukunyar.

       Idan ruwan ya tafasa sosai, sai a kwashe a zuba cikin kwatarniya /baho. Mai jego za ta yi amfani da ganyen runhu ko na darbejiya wanda za ta riƙa tsomawa cikin ruwan zafin nan tana fyaɗawa a jikinta.

       Haka za ta yi ta yi har ruwan ya ƙare.

Ana yin wankan jego ne na kimanin kwana arba’in ko wata biyu. Wannan ya danganci al’adun wurin da take.

Candidates’ performance on this question was good
Powered by Sidmach Technologies(Nigeria) Limited .
Copyright © 2015 The West African Examinations Council. All rights reserved.