waecE-LEARNING
Hausa Paper 2, May/June 2013  
Questions: 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 Main
General Comments
Weakness/Remedies
Strength
Conclusion
Question 8

Bayyana yadda ake yin wasan tahen “Zuciyar mai tsumma”

_____________________________________________________________________________________________________
Observation

This question was taken from the book Wasannin Tashe (Oral Drama).  Candidates  were required to explain how the play Zuciyar mai tsumma is staged.
Thus:                            
                       
(8)  Tashen zuciyar mai tsumma, tashe ne na yara maza. Yara kimanin shida ke
yin wannan tashen. Ɗaya daga cikinsu zai yi shigar tsummokara, ya shafa baƘin tukunya ko zargina a fuskarsa ya wuce gaba saura na biye. Idan sun je wurin da za su yi tashen, sai mai tsummokaran ya tsaya wuri guda ya yi shiru. Ɗaya daga cikinsu zai sa waƙa, sauran yara suna amsawa, kamar suna yi masa zambo.

       Waƙa:   Zuciyar mai tsumma
       Amshi:  A kusa take
       Waƙa:   Tumbuna yau salla
       Amshi:  A kusa take
       Waƙa:   Zuciyar mai tsumma
       Amshi:  A kusa take
       Waƙa:   Malam ka sani kuwa?
       Amshi:  A kusa take
       ----------------------------------
       ----------------------------------
      -----------------------------------
      Haka za su ci gaba da yi har sai an ba su sadaka.

      Few candidates attempted the question and their performance was fair.
Powered by Sidmach Technologies(Nigeria) Limited .
Copyright © 2015 The West African Examinations Council. All rights reserved.