waecE-LEARNING
Hausa Paper 2, May/June 2013  
Questions: 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 Main
General Comments
Weakness/Remedies
Strength
Conclusion
Question 2

Yi bayanin yadda ake furta biyu daga cikin waɗannan, tare da nuna siffofin furuci uku na kowanne:

  1. /m/;
  2. /t/;
  3. /l/;
  4. /g/.

Explain the articulation of any two of the following consonants and show the three points of articulation for each of them.
       (a)  /m/   (b)   /t//     (c)    /l/     (d)   /g/

_____________________________________________________________________________________________________
Observation

The question is on phonology and candidates were required to explain how any two of the above sounds are  articulated and further show their points of articulation.
Thus: 
     
a. Yayin furucin /m/, leɓen sama da na ƙasa ke haɗuwa su rufe rif, sai su tare iskar huhu mai fitowa waje, daga nan sai su saki juna iskar ta fita ta hanci. Haka kuma tantanin maƙwallato yana kaɗawa ya samar da ziza. Don haka,/m/ -  baleɓe ɗan hanci mai ziza.

b. Yayin furucin /t/, tsinin harshe ke haɗuwa da hanƙa, sai su tare iska na ɗan lokaci, sannan su saki juna iskar ta fice. Amma kuma, tantanin maƙwallato kan saki iska ta fice ba tare da karkarwa ba. Don haka, /t/ - bahanƙe tsayau maras ziza ne.

c.  Yayin furucin /l/, tsinin harshe ke haɗuwa da hanka. Mafurta kan toshe mafitar  iska na ɗan lokaci kaɗan kafin su ware, iskar ta fice ta gefen harshe. Don haka, /l/ bahanƙe ɗan jirge mai ziza.

d.  Yayin furta/g/, doron harshe ke haɗuwa da hanɗa su datse iska, sannan ta fice tare da karkarwar tantanin maƙwallato . Don haka, /g/ bahanɗe tsayau mai ziza ne.

 Few  candidates attempted the question and their performance was poor.

Powered by Sidmach Technologies(Nigeria) Limited .
Copyright © 2015 The West African Examinations Council. All rights reserved.