Hausa WASSCE (SC), 2016

Question 11

(a) Wace wasika Zaliha ta rubuta wa Dantakarda?
(b) Wane martini goggo ta bayar da ta ji cewa Zaliha ba ta son Dantakarda?

Observation

This question was taken from the book Kulba na Barna (Written Drama) and the candidates were expected to explain the type of letter Zaliha wrote to Dantakarda with the kind of response given by Goggo when she heard that Zaliha did not  love Dantakarda any longer.

Thus:
(a). Bayan Alhaji Ruwan Ido ya hure mata kunne, tare da cewa aurenta zai yi, sai Zaliha ta rubuta wa Ɗantakarda wasiƙa cewa ta canja ra’ayinta game da shi.
Ga abin da ta rubuta :
Zuwa ga Ɗantakarda,  bayan haka , abin da ya sa na rubuta maka wannan
wasiƙa domin in sanar da kai tun da wuri don kada in ƃata maka  lokaci.  Ni
abin da zan gaya maka shi ne, ni dai ba wai ƙaunar ka ce ba na yi ba, ina
son tun da wuri ka samu matar da za ka aura.  Ni yanzu sai mai rabo.  To,
ina son ka, daure ka same mata  fun da wuri.  Ni kani, na canya ra‘ayina
yanzu  na samu mijin aure.  Saboda haka, daga yau, da ni da kai babu
sauran so. Ka huta lafiya.. Ni ce taka Zaliha Bankani.

 

(b). Martanin da Goggo ta bayar, shi ne, ‘To, Allah ya ƙara, Allah ya saƙe ƙarawa! Ai wallahi ba ya da kaico.  Ai yanzu ka ga waƙwabta sun sami abin yi masa  dariya ke nan.  Da ma ai sai da na faɗa masa  na ce in dai har shi bai ce ba ya son ta ba, to ita ta ce  ba ta son sa.  Abin da ni na san halin ‘yan boko  ba tun yau ba.  Wallahi, Allah ya ƙara masa Akawu.  Nan wurin ba wanda bai ji ina faɗa masa cewa ya kiyayi Zaliha ba, amma yaron nan ya liƙe mata sai ka ce kaska, wai sai ya aure ta.

 

Candidates’ performance on this question was fair.